Addini
Alhazan Najeriya Za Su Fara Dawowa Gida a Yau Laraba
Za a fara jigilar alhazan Najeriya da suka halarci aikin Hajjin bana zuwa gida a yau Laraba 03 ga Yuni, inda alhazan Jihar Nasarawa za su kasance na farko. Kamfanin jirgin sama na Flynas ya ce alhazan jihohin Ogun da Kebbi za su biyo baya a ranar 4 ga Yuni.
Kamfanin ya bayyana cewa zai yi amfani da manyan jirage shida kirar A330 domin tabbatar da jigilar alhazan cikin sauki da tsari. Jiragen farko za su tashi daga filin jirgin saman Jeddah zuwa Abeokuta da Birnin Kebbi dauke da rukuni na farko na alhazan jihohin Ogun da Kebbi.
Shugaban kamfanin First Planet Travels Limited, Alhaji Umar Kaila, ya ce Flynas ta yi jigilar alhazai da jami’ai 11,342 zuwa kasa mai tsarki cikin jirage 30 a cikin makwanni biyu kacal. Kakaki24 ta ruwaito cewa kamfanin ya kuma tura kwalaben ruwan Zamzam 13,832 zuwa Najeriya gabanin dawowar alhazan daga aikin Hajji.
