Featured
NSCDC Ta Daƙile Wani Yunƙurin Garkuwa da Mutane a Kano
Jami’an Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Kano sun yi nasarar dakile wani yunkurin sace mutane da kuma satar shanu a yankin Bakin Komau da ke Dangora a Karamar Hukumar Kiru. Lamarin ya faru ne ranar Alhamis lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka kai hari kan wani makiyayi.
A cewar kakakin hukumar, SC Ibrahim Abdullahi, maharan sun jikkata makiyayin mai shekaru 70, Alhaji Saleh, sannan suka yi awon gaba da ’ya’yansa biyu yayin da suke kokarin kwashe dabbobi. Bayan samun rahoton gaggawa, jami’an NSCDC suka garzaya wurin tare da fafatawa da maharan.
Maharan sun tsere zuwa cikin daji bayan sun kasa cimma manufarsu, inda suka bar wadanda suka sace. An ceto Abubakar Saleh mai shekaru 36 da Muhammad Inuwa Dille mai shekaru 30 tare da mayar da su ga iyalansu. Kakaki24 ta rawaito cewa hukumar NSCDC ta sake tabbatar wa al’ummar Kano kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi tare da kira ga jama’a su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
