Featured
Ƴansanda Sun Ceto Ƴar Uwar Tsohon Ministan Lantarki da Aka Sace a Ibadan
Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Najeriya sun ceto Olaide John-Paul, ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, tare da tagwayen ’ya’yanta masu shekara 12, Peter da Paul, bayan wani samame da suka kai a Ibadan.
An sace su ne a ranar 3 ga Yunin 2026 yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makaranta a jihar Oyo. Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun bi sawunsu tun daga gida kafin su tare su tare da yin awon gaba da su.
Bayanai sun nuna cewa jami’an tsaro sun gano inda aka tsare su tare da gudanar da farmaki da ya yi sanadin kashe masu garkuwa biyu tare da kama wasu biyu. Kakaki24 ta ruwaito cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo ya tabbatar da cewa an ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya ba tare da sun samu wata illa ba.
