Featured
Hukumar Zaɓe a Bauchi Ta Sanar da Ranar Gudanar da Zaɓukan Kananan Hukumomi
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC) ta sanar da ranar 17 ga Agustan 2026 a matsayin ranar gudanar da zaben kananan hukumomin jihar, tare da fitar da sanarwar kwanaki 60 kamar yadda doka ta tanada.
Sakataren hukumar, Nuru Abdulhamid, ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da tanade-tanaden dokar zaben jihar, wadda ta wajabta sanar da jam’iyyun siyasa, masu ruwa da tsaki da kuma jama’a kafin gudanar da zabe.
Hukumar ta bukaci jam’iyyun siyasa da ke shirin shiga zaben da su kammala shirye-shiryensu tare da bin dokoki da ka’idojin zabe. Ta kuma jaddada kudirinta na gudanar da sahihin zabe mai gaskiya, adalci. – Kakaki24
