Addini
Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Musanta Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare-Dangi a Najeriya
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce babu hujjar da ke nuna ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, tana mai bayyana cewa matsalar rashin tsaro da hare-haren ’yan ta’adda na shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ba.
Babbar jami’ar MDD mai kula da harkokin ’yancin addini, Nazila Ghanea, ta bayyana hakan bayan wata ziyara da tawagarta ta kai Najeriya, inda suka tattauna da mutane sama da 200 a Abuja, Kano da Jihar Filato. Ta ce binciken ya nuna cewa Musulmi da Kiristoci dukkansu na fuskantar matsaloli iri ɗaya.
Nazila ta ƙara da cewa ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi a arewacin Najeriya sun fi kashe Musulmi fiye da Kiristoci a yankunan da suke kai hare-hare. Kakaki24 ta ruwaito cewa MDD ta jaddada buƙatar ɗaukar matakai masu ƙarfi kan masu aikata laifuka domin kare rayuka da tabbatar da ’yancin addini a ƙasar.
