Featured
Ƙudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Isa Gaban Majalisun Jihohi
Najeriya ta kara matsowa kusa da kafa rundunar ’yan sandan jihohi bayan da Majalisar Dattawa ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman bai wa jihohi damar kafa nasu rundunar tsaro. Yanzu hankula sun koma kan majalisun dokokin jihohi 36, inda ake bukatar aƙalla jihohi 24 su amince da kudirin kafin ya zama doka.
Kudirin ya tanadi ci gaba da kasancewar rundunar ’yan sandan tarayya tare da kafa rundunar ’yan sandan jihohi, yayin da gwamnoni za su rika naɗa kwamishinonin ’yan sanda na jihohinsu bayan amincewar majalisun dokokin jihohi. Haka kuma an saka matakan kariya domin hana amfani da rundunar wajen danniya ko takurawa masu adawa da gwamnati.
Read Also: Rundunar Ƴan Sanda Ta Musanta Zargin Alaƙa Da Ƴan Bindiga a Katsina
Masu goyon bayan kudirin sun ce zai taimaka wajen inganta tsaro da tattara bayanan sirri a matakin al’umma, yayin da masu adawa ke nuna fargabar yiwuwar amfani da rundunar wajen siyasa. Idan majalisun jihohi suka amince da shi, za a miƙa kudirin ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sanya hannu ya zama doka.
