Featured
Jarrabawar NECO : Ɗalibai 36 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Har Yanzu Suna Hannun Ƴan Bindiga – Rundunar Ƴansanda
‘Yan sandan Najeriya sun tabbatar da cewa har yanzu ɗalibai 36 tare da wani ma’aikacin makaranta guda ɗaya na hannun ‘yan bindiga, bayan harin da suka kai ranar Litinin a lokacin da ɗaliban ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO a jihar Borno.
‘Yan sandan sun ce sun tantance adadin mutanen da aka sace, kuma jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto. Haka kuma, an riga an kuɓutar da mutane 10 ciki har da mataimakin shugaban makarantar.
Read Also : Tinubu Ya Amince Da Aikin Tituna 27 Akan Naira Tiriliyan 3.9
An kai harin ne a garin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira Uba. Kakaki24 ta ruwaito cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike a dazukan da ke maƙwabtaka da yankin domin gano inda waɗanda aka sace suke tare da kuɓutar da su.
