Featured
Kotu Ta Bayar da Belin Dr Bashir Kurfi
Babbar Kotun Majistare da ke Jihar Katsina ta bayar da belin masani kan harkokin tsaro kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, Dakta Bashir Kurfi, bayan gurfanar da shi bisa zargin bata suna. An ba shi belin ne bayan ya bayyana a gaban kotun domin amsa tuhume-tuhumen da ake masa.
Lauyan wanda ake kara, Barista A.D. Umar, ya ce zaman kotun ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma ya yaba da matakin da kotun ta ɗauka. Ya bayyana cewa bangarorin masu kara da masu kare wanda ake zargi sun gamsu da yadda aka gudanar da shari’ar.
Read Also : Gov. Yusuf Nominates Garo as Running Mate for 2027 Re-election Bid
Kotun ta gindaya sharadin gabatar da mutane biyu mazauna Jihar Katsina masu kadarar ƙasa a matsayin masu tsaya masa, tare da Naira 500,000 kan kowane ɗaya idan ya gaza halartar kotu. Daga nan kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga Agustan 2026, yayin da Bashir Kurfi ya musanta zarge-zargen da ake masa.
