Connect with us

Featured

FRSC za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da ya hana ta aiki a titunan jiha a Kano

Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Kano ta yanke na hana jami’anta gudanar da aiki a hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi, tare da taƙaita aikinsu zuwa manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.

Kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a M. S. Shuaibu, ta yanke hukuncin ne bayan ƙarar da Barrista Abba Hikima ya shigar. Kotun ta ce jami’an FRSC sun wuce iyakokin ikon da doka ta ba su ta hanyar kafa shingayen bincike a hanyoyin cikin birnin Kano ba tare da direbobi sun aikata laifin hanya ba, tare da umartar hukumar ta biya diyyar naira 800,000 da kuma wallafa neman afuwa a jarida.

Read Also : Kotun Ƙoli Ta Bayar da Umarnin Ƙwace Kadarori 7 Na Emefiele

Da take martani, FRSC ta ce tana mutunta hukuncin kotun amma an yi masa mummunar fassara a tsakanin jama’a. Hukumar ta ce hukuncin bai soke ikon da dokarta ta ba ta ba, sai dai ya taƙaita aikinta a Kano zuwa hanyoyin gwamnatin tarayya, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa doka yayin da take jiran sakamakon ɗaukaka ƙarar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet