Featured
Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Kamfanin Jiragen Sama Mallakin Jihar
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatinsa na kafa kamfanin jiragen sama mallakin jihar domin samar da ayyukan yi ga matukan jirgi ‘yan asalin Kano da suka kammala horo.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karo na 40 da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, inda ya ce ana sa ran kamfanin jiragen saman zai fara aiki nan da shekara guda mai zuwa, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta samar da dukkan goyon bayan da ake buƙata domin ganin shirin ya yi nasara.
Read Also : Kotu Ta Yanke Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai Ga Mutanen da Suka Sace Ɗaliban Oyo
Ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda matukan jirgin da gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin horas da su a ƙasar Jordan suka yi fice, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ɓangaren sufurin jiragen sama tare da samar musu da damar ba da gudunmawa ga ci gaban jihar.
A nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Matukan Jiragen Sama ta Jihar Kano, Naziru Ibrahim, ya yaba wa gwamnan bisa taimakon da ya bayar wajen sabunta lasisin tashi na mambobinsu, sannan ya roƙi gwamnatin da ta ƙara tallafa musu wajen samun takardun shaidar ƙarshe da za su ba su damar gudanar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci a Najeriya da ƙasashen waje.
