Featured
Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Kan Yawan Ciwo Bashi
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rasa ikon kula da harkokin kuɗin Najeriya.
Atiku ya ce gwamnatin tarayya ta ciwo bashin da ya haura adadin da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da shi da Triliyan ₦4.79 a shekarar 2024, lamarin da ya kai sabon bashin zuwa Triliyan ₦12.62.
Read Also : Ƴan Bindiga Sun Kashe Kanal Ɗin Soja a Nasarawa
Ya ce cire tallafin man fetur, ƙarin haraji da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da aka ce za su rage dogaro da bashi, sun haifar da akasin haka. Atiku ya kuma ce bashin bai nuna tasiri sosai a fannin ilimi, lafiya, tsaro da ababen more rayuwa ba.
Atiku ya ce rahoton Ofishin Kasafin Kuɗi ya nuna cewa hidimar bashi ta kai Triliyan ₦12.36, sama da hasashen kasafin kuɗi da fiye da kashi 52. Ya buƙaci a mayar da hankali kan rage ɓarna, toshe ɓoyayyun hanyoyin asarar kuɗi da amfani da dukiyar ƙasa wajen bunƙasa tattalin arziki.
