Addini
Ƴar Najeriya Ta Lashe Naira Miliyan 120 a Musabaƙar Alƙur’ani ta Saudiyya
Maryam Danazimi Ibrahim daga Najeriya ta lashe kyautar Naira miliyan 120, kwatankwacin Riyal 300,000 na Saudiyya, bayan ta zo ta farko a rukunin mata a gasar Alƙur’ani ta Sarki Abdulaziz da aka gudanar a Makka.
Danazimi, wadda ta fito daga jihar Gombe, ta yi nasara a rukunin da ya ƙunshi haddar Alƙur’ani gaba ɗaya tare da kyakkyawar karatu da Tajwid, da kuma fassarar ma’anonin kalmomin Alƙur’ani.
Read Also : Matuƙar aka yi zaɓe na gaskiya kafin 4 na yamma Tinubu ya faɗi – Baba Ahmed
Ta kasance cikin ’yan takara 50 da suka yi nasara a rukuni biyar na gasar, waɗanda suka haɗa da maza 25 da mata 25. Gasar ta samu halartar ’yan takara 334 daga ƙasashe 133 na duniya.
Gasar ta bana ita ce karo na 46, kuma ita ce ta farko da aka bai wa mata damar shiga gasar ta ƙasa da ƙasa. Gabaɗaya, mata 132 da maza 202 ne suka fafata, yayin da kyaututtukan gasar suka kai Riyal miliyan 10.26.
