Featured
Mutane 40 Sun Mutu Bayan Wani Kwale-kwale Ya Kife a Sokoto
Akalla mutum 40 ake zargin sun rasa rayukansu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da manoma zuwa gonakinsu ya kife a garin Gorau, Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne yayin da mutanen ke tsallaka wani rafi domin zuwa gonakin shinkafarsu. Rahotanni sun ce mafi yawan waɗanda ke cikin jirgin yaran ne masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15.
Wani ganau ya ce sama da mutum 70 ne ke cikin jirgin lokacin da ya kife jim kaɗan bayan tashi. Ya ce an ceto mutum shida, ciki har da shugaban ƙauyen, yayin da aka gano gawarwaki kusan 40.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da masu gonaki da ma’aikatan da aka ɗauka domin girbin shinkafa. A halin yanzu, aikin ceto na ci gaba, inda masu ruwa na yankin ke neman waɗanda suka ɓace tare da kwashe gawarwakin.
