Addini
Hajjin 2027: Gwamnan Kano Ya Naɗa Sarkin Rano Amirul Hajj
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, a matsayin Amirul Hajj na jihar Kano a aikin Hajjin shekarar 2027.
Gwamnan ya sanar da naɗin ne yayin ziyararsa masarautar Rano ranar Juma’a 21 ga Agusta, 2026, inda ya halarci bikin ɗaurin auren ɗan fari na Sarkin, Muhammad Abubakar Isa, tare da bikin naɗa shi sarauta.
A cewar sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar, Yusuf ya ce naɗin ya yi daidai da tsarin jihar na sauya jagorancin tawagar aikin Hajji tsakanin masarautun jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa Sarkin Gaya, Alhaji Dakta Abdulkadir Ibrahim, ne ya jagoranci tawagar jihar a aikin Hajjin da ya gabata, don haka Sarkin Rano ne zai jagoranci aikin Hajjin 2027. Sarkin Rano da ’yan masarautarsa sun gode wa gwamnan, tare da bayyana naɗin a matsayin babban abin alfahari.
