Connect with us

Featured

Wasu ƴan Najeriya sun roƙeni na rage wutar lantarkin da muke samarwa saboda firinjinsu ya fara daskarewa – Ministan Lantarki

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa wasu masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya sun roƙe shi da a ɗan rage lantarki da ake basu, saboda firinjinsu ya fara daskarewa, yace sun fadi haka ne sakamakon gagarumin ci gaban da aka samu wajen samar da wutar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da aikin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin megawatt 3 a Jami’ar Abuja.

Read Also : Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci Ta Jihar Kano Ya Yi Murabus 

Tegbe ya ce wasu wuraren da suka shafe watanni uku ba tare da wuta ba, yanzu suna samun wutar lantarki har na tsawon sa’o’i 18. Ya kuma ce wasu daga cikin kayayyakin samar da wutar lantarki a Najeriya sun haura shekaru 40, amma yanzu gwamnati na maye gurbinsu da sababbi.

Ministan ya kuma bayyana damuwarsa kan lalata muhimman kayan aikin wutar lantarki, inda ya ce ɓata gari sun rushe hasumiyoyin rarraba wuta guda uku a Birnin Kebbi. Ya ce gwamnati ta kafa kwamitin haɗin gwiwa da ya ƙunshi EFCC, ’Yan Sanda da NSCDC domin kare kadarorin wutar lantarki da kuma yaƙi da ɓata gari.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: PDP ta sauya sunan ɗan takarar gwamnan Kano da Muhammad Sani Abacha - KAKAKI 24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinovdcasinoholiganbetmarsbahissahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet