Featured
PDP Ce Jam’iyyar Da Ta Yi Dai-dai Da Al’ummar Najeriya; Idan Mun Yi Nasara, Za Mu Yi Muku Adalci — Garba Dogo
Daga Sani Gazas Chinade, Azare
Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Katagum, Hon. Muhammad Garba Dogo Dan Amar, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ta fi dacewa da al’ummar Najeriya, yana mai cewa jam’iyyar tana da matsayi na musamman a zukatan jama’a.
Garba Dogo, wanda ke neman kujerar ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa a wani taro da aka gudanar a ɗakin taro na Oricon Hotel da ke Azare.
Ya ce tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, PDP ta taka muhimmiyar rawa a siyasar ƙasar, yana mai cewa idan aka ba su dama ta hanyar zaɓe, za su yi wa al’umma adalci.
“Idan mun yi nasara, za mu yi muku adalci, insha Allah,” in ji Garba Dogo.
Taron ya samu halartar wasu daga cikin manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga ƙananan hukumomin Katagum, Shira da Toro, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdu Kuda, tsohon shugaban ƙaramar hukumar.
A cewar Garba Dogo, PDP ta samu gagarumar nasara a tarihin siyasar Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya, yana mai cewa jam’iyyar ta samar da ci gaba ga jama’a da ƙasa baki ɗaya.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa kan samun nasarar jam’iyyar a zaɓukan da ke tafe, tare da kira ga magoya bayansa da su ƙara ƙoƙari wajen ganin an samu nasara.

Ɗan takarar ya kuma yi kira ga al’ummar mazabar Katagum da su fito a lokacin zaɓe domin zaɓensa a matsayin wakilinsu a Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Ya ce yana da shirin samar da wakilci mai inganci idan aka ba shi damar wakiltar mazabar, tare da kira ga jama’a da su mara wa sauran ’yan takarar jam’iyyar PDP baya a matakai daban-daban.
Garba Dogo ya bayyana cewa, a wani mataki na ƙara ƙarfafa kamfen ɗin, ya kafa kwamitin mambobi 37 da zai gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na ƙaramar hukumar Katagum tare da hulɗa da jama’a kan manufofin kamfen ɗin.
Ya buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da ayyukansu bisa ƙwazo da sanin ya kamata domin cimma manufofin da aka ɗora musu.
Haka kuma, ya isar da saƙon ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, Alhaji Usman Suphi, wanda ya yi kira ga jama’a da su zaɓi ’yan takarar jam’iyyar a matakai daban-daban.
Tun da farko, yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kwamitin, mai kula da kwamitin dabarun zaɓe, Alhaji Yahya Muhammad Gadauji, ya tabbatar wa Hon. Garba Dogo cewa kwamitin zai yi aiki tukuru wajen ganin an cimma nasarar jam’iyyar da kuma ɗan takarar.

Pingback: Kano Online Media Chapel Approves New Revenue Measures - KAKAKI 24