Featured
Dangote da Ƴan Kasuwa Sun Rage Farashin Fetur Bayan Saukar Farashin Ɗanyen Mai a Kasuwannin Duniya
Matatar Man Fetur ta Dangote da wasu ‘yan kasuwar man fetur sun rage farashin fetur a manyan tashoshin rarraba mai na Legas, Fatakwal, Kalaba da Warri, sakamakon raguwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
A Legas, matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N1,350 zuwa N1,325, yayin da Ascon, Integrated, Pinnacle da Sahara suka rage N24 akan yadda suke sayarwa. MRS ma ta rage farashin daga N1,352 zuwa N1,332 kan kowacce lita.
A Fatakwal, Masters ya rage farashin zuwa N1,328, yayin da Stockgap ya koma N1,323. A Kalaba kuwa, Mainland ya rage farashin zuwa N1,320, wanda shi ne mafi sauki cikin wuraren da rahoton ya rufe.
Raguwar farashin ya zo ne yayin da danyen man Brent ya sauka zuwa dala 99.77 kan ganga, yayin da WTI ya koma dala 91.17. Rahoton ya ce farashin fetur a gidajen mai yanzu yana tsakanin N1,370 da N1,450, gwargwadon wuri.

Pingback: Zaɓen 2027 tsakanin APC da ƴan Najeriya za a yi shi – Makinde - KAKAKI 24