Connect with us

Featured

Gwamna Buni Ya Sake Nada Mai Aliyu A Matsayin Mukaddashin Shugaban Hukumar Alhazai ta Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya amince da sake nada Alhaji Mai Aliyu a matsayin mukaddashin Shugaban gudanarwa na hukumar alhazai ta Jihar Yobe.

Sakataren gwamnatin Jihar Yobe (SSG), Dr. Mohammed Goje ne ya gabatar da takardar nadin ga Mai Aliyu a madadin Gwamna Buni.

Kamar yadda sanarwar ta jaddada nadin zai fara aiki daga ranar 7 ga Oktoba, 2026, har sai majalisar dokokin Jihar Yobe ta tabbatar da shi.

A cewar wasikar, sake nadin ya nuna amincewar Gwamna ga cancantar Mai Aliyu, ƙwarewa da jajircewarsa ga aiki.

PCACC Arrests Suspect Over Alleged Illegal Sale of Government Horse Stable in Kano

Wasikar ta bukaci mukaddashin Shugaban da aka sake nada wa ya yi kokarin sauke nauyin da aka dora masa tare da himma, mutunci da kuma sadaukarwa, domin ya tabbatar da amincewar da Gwamna ya yi masa a bisa cancantar sa.

Sakataren gwamnatin jihar, yayin da yake gabatar da takardar nadin, ya taya Mai Aliyu murna tare da yi masa fatan samun nasara wajen sauke nauyin da ke kansa.

Sake nadin Mai Aliyu ya zo ne a dai-dai lokacin da gwamnatin Buni ke ci gaba da kokarinta na karfafa gudanarwa da gudanar da harkokin aikin hajji a jihar.

Majalisar dokokin Jihar Yobe za ta tabbatar da nadin na sa nan gaba da zarar ta zauna.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet