Featured
Mutane 3 sun mutu, da dama sun jikkata yayin turmutsitsin jama’a a Gidan Gwamnatin Neja
Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon turmutsitsin jama’a da ya faru a Gidan Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna.
Lamarin ya faru ne a daren Talata, bayan wasu matasa da ake zargin suna shirin gudanar da zanga-zanga kan mutuwar masu hakar ma’adinai 37 sun je Gidan Gwamnatin. Daga cikin wadanda suka mutu akwai wata mata mai suna Dije da diyarta Hurairat.
Read Also : Emir Bayero Condemns Destruction of Kano Governor’s Banners, Orders Immediate Replacement
An bayyana cewa Dije da Hurairat ‘yan gudun hijira ne daga garin Allawa a Karamar Hukumar Shiroro. An ce sun je Gidan Gwamnatin ne bayan sun ji cewa Gwamna Mohammed Umaru Bago, zai raba kudi ga mutanen da suka hallara a wajen.
Kakakin Gwamnan Neja, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnati za ta fitar da sanarwa kan lamarin, yayin da ‘yan sandan jihar ke cigababda gudanar da bincike kan lamarin.

Pingback: Ina cikin ƙoshin lafiya kuma a shirye nake na cigaba da aiki gadan-gadan - Tinubu - KAKAKI 24