Featured
Tinubu Ya Ayyana Makokin Kwanaki Uku Sakamakon Mutuwar Jami’an Sojin Sama
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku sakamakon hatsarin jirgin soji da ya yi sanadin mutuwar mutane 32 a jihar Ondo.
Tinubu ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, tare da umartar a sauke tutocin Najeriya ƙasa domin girmama jami’an sojin da suka rasu.
Read Also : Tragedy In Yobe As CMD FMC Nguru Loses Twin Daughters 3 Days Apart
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai da suka rasu.
Shugaban ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga Rundunar Sojin Sama da ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa ba za a taɓa mantawa da sadaukarwar jami’an da ke jefa rayukansu cikin haɗari domin kare Najeriya ba.
