Featured
Harin Sojojin Masar Ya Kashe Masu Haƙar Zinare 72 a Sudan
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Sudan, Emergency Lawyers, ta zargi sojojin saman Masar da kai hari kan wani wurin haƙar zinare kusa da kan iyakar Sudan da Masar, inda ta ce an kashe aƙalla masu haƙar zinare 72.
Waɗanda suka tsira daga wurin haƙar ma’adinan na Al-Uqayadat sun ce akwai yiwuwar adadin waɗanda suka mutu ya fi haka a harin da ya faru a ranar Asabar.
Read Also : Ƙididdigar da muka yi ta nuna cewa Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 – APC
Wakilin BBC ya ce harin ya biyo bayan wani harin sama da aka kai a watan Yuni, wanda shi ma ake zargin Masar da kai wa, inda aka ce an kashe ma’aikata 23.
A wancan lokacin, rundunar sojin Masar ta bayyana cewa ta kai farmaki ne kan masu haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba. Sai dai ya zuwa yanzu, Masar ba ta yi wani martani kan sabbin zarge-zargen ba.

Pingback: Sabon Harin Houthi Ya Kashe Mutum Ɗaya a Filin Jirgin Sama na Riyadh - KAKAKI 24