Connect with us

Featured

Mayaƙan RSF Sun Ƙwace Birnin El-fasher Na Sudan

Khartoum, Sudan – Shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya tabbatar da cewa dakarun ƙasar sun janye daga wuri na ƙarshe da ke ƙarƙashin ikon su a yammacin El-Fasher, domin kauce wa rugujewar wurin gaba ɗaya, a yayin da mayaƙan Rapid Support Forces (RSF) suka mamaye birnin.

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu akwai dubban sojojin gwamnati da mayakan RSF suka yi wa kawanya a wajen da ke yammacin birnin.

RSF dai ta musanta zarge-zargen da ake yadawa cewa tana kashe fararen hula, sai dai kungiyoyin agaji sun nuna fargaba cewa ana iya aikata kisan kiyashi a kan kabilun da ba Larabawa ba, waɗanda suka makale a cikin birnin.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana cewa kawanyar da aka yi wa El-Fasher tsawon watanni 18 ta jefa mazauna yankin cikin mummunan hali na yunwa, cututtuka da tashin hankali sakamakon ci gaba da faɗan da ake yi.

Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta mutane dubu 26 sun tsere daga El-Fasher cikin kwana biyu da suka gabata, abin da ke nuna cewa mutanen da suka rage a birnin yanzu ba su wuce kashi 10 cikin 100 ba na yawan mazauna da ke can a da.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet