Featured
NELFUND Ta Raba Tallafin Biliyan 116.4 Ga Ɗalibai Fiye Da 624,000 a Najeriya
Hukumar bayar da tallafin karatu ta Najeriya, NELFUND, ta bayyana cewa ta rarraba sama da naira biliyan ₦116.4 ga ɗalibai 624,535 tun bayan buɗe shafin neman tallafin a ranar 24 ga Mayu, 2024. Rahoton da hukumar ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, ya nuna cewa an karɓi aikace-aikace 929,805, inda sabbin ɗalibai 12,398 suka samu nasarar shiga cikin jerin masu cin gajiyar shirin.
A cewar rahoton, hukumar ta biya naira biliyan ₦65.3 a matsayin kuɗin makaranta ga manyan makarantun gwamnati 239, sannan biliyan ₦51.1 ta shiga hannun ɗalibai a matsayin kuɗin rayuwa (upkeep allowance). Wannan ya kai jimillar kuɗin da aka fitar zuwa ₦116.4bn.
NELFUND ta kuma sanar da cewa an buɗe sabon shafin neman tallafin karatu na shekarar 2025/2026 tun a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba 2025 zuwa Asabar, 31 ga Janairu 2026. Hukumar ta shawarci sabbin ɗalibai da su yi amfani da lambar JAMB ko ta shaidar shiga jami’a (Admission Number) wajen cike fom.
An kafa hukumar NELFUND ne a ƙarƙashin dokar shirin lamunin ɗalibai da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kai a Afrilu 2024. Shirin yana bai wa ɗaliban makarantun gwamnati lamuni ba tare da riba ba, domin biyan kuɗin makaranta da tallafin rayuwa, musamman ga waɗanda ke da ƙarancin ƙarfi. Ana sa ran masu cin gajiyar za su biya bayan kammala karatu da samun aiki.
