Featured
Sabon Harin Houthi Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Ɗaya a Filin Jirgin Sama na Riyadh
Hukumomin Saudiyya sun ce harin da ’yan tawayen Houthi na Yemen suka kai a jiya Lahadi kan babban filin jirgin sama na Riyadh ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu 11.
Wannan shi ne karo na uku da aka kai hari kan filin jirgin saman cikin kwanaki huɗu. Inda harin da aka kai ranar Asabar ya yi sanadin mutuwar mutane 13.
Read Also : Harin Sojojin Masar Ya Kashe Masu Haƙar Zinare 72 a Sudan
Ƙungiyar Houthi ta ce ta kuma kai hari kan filin jirgin saman Dammam da ke gabashin Saudiyya, tare da wasu wuraren da ake sarrafa man fetur.
Wakiliyar BBC ta ce ƙarin tashin hankalin na iya ƙara assasa damuwar da ake da ita kan batun fitar da ɗanyen mai daga wannan yankin zuwa sassan duniya.

Pingback: Ƴan bindiga sun hallaka sojoji 8 da fararen hula 4 a Zamfara - KAKAKI 24