Connect with us

Featured

Rundunar ƴan sandan Kano ta yi alkawarin tabbatar da Tsaro yayin zaɓen 2027

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar za ta samar da ingantaccen tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen 2027. Ya kuma buƙaci jami’an yaɗa labarai su taimaka wajen yaƙi da labaran ƙarya da bayanan da za su iya tayar da zaune tsaye.

Bakori ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, yayin taron shekara-shekara na Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR), reshen Kano, da aka gudanar a Tahir Guest Palace. Taken taron shi ne “Gudanar da Sakamakon Zaɓe: Rawar Jami’an Yaɗa Labarai.”

Read Also : Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci

Kwamishinan ya ce ingantattun bayanai na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da amincewar al’umma ga hukumomi. Ya kuma bayyana cewa rundunar za ta yi aiki bisa tsarin IGP Olatunji Rilwan Disu, tare da tattara bayanan sirri da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Ya buƙaci jami’an yaɗa labarai su fifita sahihanci a kan gaggawa wajen yaɗa sakamakon zaɓe, tare da kauce wa kalaman ƙiyayya da labaran ƙarya. A nasa ɓangaren, Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Zango Abdu, ya ce hukumar na shirin gudanar da zaɓe mai ’yanci, adalci da gaskiya a 2027.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Zaɓen 2027: Arewa za ta bai wa Tinubu ƙuri’u fiye da na 2023 — Shettima - KAKAKI 24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet