Connect with us

Featured

Za a iya ɗage zaɓen 2027 idan Ebola ta cigaba da yaɗuwa a Najeriya – NCDC

Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta ce za a iya ɗage babban zaɓen 2027 idan cutar Ebola ta cigaba da yaɗuwa a ƙasar zuwa matakin da hakan zai zama dole domin kare lafiyar jama’a.

Darakta-Janar na NCDC, Dr Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Channels Television. Ya ce girman matsalar da kuma yadda cutar za ta yaɗu a sassa daban-daban ne za su iya tabbatar da ko ya dace a ɗage zaɓe, ko kuma a gudanar da shi.

Read Also : INEC ta sanya ranar bayyana makomar Pantami, Gwarzo da Adebutu

Sai dai Idris ya ce a halin yanzu babu wani dalilin tunanin ɗage zaɓen, yana mai fatan za a shawo kan cutar ba tare da ta kawo cikas ga jadawalin zaɓen ba. Ya kuma ce duk wani mataki na ɗage zaɓen zai kasance ne bisa la’akari da lafiyar jama’a, ba siyasa ba.

Ya bayyana cewa Najeriya na sa ido kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda cutar ta samo asali, tare da lura da zirga-zirgar jama’a, jiragen sama da mashigai. Idris ya jaddada cewa jami’an lafiya ba za su yi amfani da cuta a matsayin makamin siyasa ba.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Gwamnan Kano Ya Yi Barazanar Korar Duk Jami’in Da Aka Kama Yana Sayar Da Kayan Tallafi - KAKAKI 24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet