Featured
Gwamnan Kano Ya Yi Barazanar Korar Duk Jami’in Da Aka Kama Yana Sayar Da Kayan Tallafi
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi barazanar korar duk wani jami’in siyasa ko ɗan jam’iyya da aka kama yana sayar da kayan tallafin ƙarfafa tattalin arzikin da aka raba wa al’umma.
Kayan tallafin dai an raba su ne ta hannun Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, domin tallafa wa al’umma.
Read Also : Za a iya ɗage zaɓen 2027 idan Ebola ta cigaba da yaɗuwa a Najeriya – NCDC
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, a wajen bikin ƙarfafa tattalin arzikin al’umma karo na 12, kamar yadda jaridar DCL ta ruwaito.
An gudanar da bikin ne a ranar Litinin, inda aka bayyana matsayar gwamnan kan duk wani jami’in siyasa ko ɗan jam’iyya da aka samu yana sayar da kayan tallafin.

Pingback: Ƙungiyar Ansaru ta dauki alhakin kisan Yahya Masussuka - KAKAKI 24