Featured
Da ɗumi ɗumi : Gwamnan Kano ya cire Waiya daga kwamishinan yada labarai
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauya wa wasu kwamishinoni ma’aikatun da suke jagoranta, tare da bayyana sabbin ma’aikatun da aka ware musu.
A sabon tsarin, an mayar da Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya zuwa Ma’aikatar Matasa, yayin da Hon. Safyanu Kachako aka mayar da shi Ma’aikatar Muhalli.
Sauran kwamishinonin da aka ware wa ma’aikatu sun haɗa da :
Hon. Yushau Soja — Tsaro
Hon. Idris Garba Mustapha — Ayyuka na Musamman
Hon. Muntari Ishaq Yakasai — Jinƙai
Hon. Ibrahim Namadi Dala — Kasuwanci
Hon. Ibrahim Tsanyawa — Kimiyya da Fasaha.
Farfesa Sani Lawal – Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi
Ibrahim Adam, hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen sada zumunta, ne ya wallafa jerin sabbin ma’aikatun da kwamishinonin za su jagoranta.
