Connect with us

Featured

Danbatta ya buƙaci gwamnan Kano ya naɗa ƙwararren ɗan jarida a matsayin kwamishinan yaɗa labarai

Wani ƙwararren ɗan jarida a Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya, Dakta Garba Ubale Danbatta, ya yaba wa Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa cire tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, daga mukaminsa.

A cikin wani saƙo da Dakta Garba Ubale Danbatta ya aikowa ‘yan jarida, ya bayyana cewa abubuwan da tsohon Kwamishinan ya riƙa yi sun fi kama da ayyukan ƙungiyoyi maimakon aikin jarida, lamarin da ya ce ya rage darajar fannin a faɗin Jihar Kano.

“A matsayin mu na wanda suka shafe fiye kimanin shekaru 30 muna aikin Jarida, muna yabawa Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusif da matakin daya dauka na cire tsohon kwamishinan yada labarai daga kujerar sa, saboda kusan ba aikin jarida yayi tayi ba, aiki yayi tayi irin na yan gwagwarmaya wanda hakan kusan a iya cewa kwamacala ce, domin yaci karo da sharruda ko kaidoji aikin Jarida,” inji Dakta Danbatta.

Ya ƙara da cewa irin abubuwan da tsohon Kwamishinan ya riƙa yi sun jawo wa Jihar Kano mummunar fahimta daga ƙungiyoyin da ke sa ido kan harkokin aikin jarida da kuma haƙƙin ‘yan jarida.

“Irin abubuwan da ya rika ya jawowa Jihar Kano mummanar fahinta da suka daga kungiyoyin dake sa ido akan harkar aiki jarida da kuma hakkin yan jarida, abun babu dadin ji,” inji shi.

Dakta Garba Ubale Danbatta ya bayyana fatan cewa a wannan karon, Gwamnan zai naɗa wanda ya cancanta, yake da ƙwarewa a fannin aikin jarida, sannan yake da kyakkyawar mu’amala da ‘yan jarida, domin kawo gyara da dawo da martabar aikin jarida a Jihar Kano.

“Matukar gwamnan Kano ya yi mana haka, mu kuma a shirye muke muci gaba da bada dukkan wata gudummawa da shawarwari da zata taimaka wajen kyautata aikin tare da daga darajar sa a Jihar Kano a idon Duniya,” inji Danbatta.

Garba Ubale Danbatta dai ya shafe sama da shekaru 30 yana aikin jarida a ciki da wajen Najeriya.

Dakta Danbatta ya yi aiki da Sashen Hausa na DW Hausa da ke birnin Bonn, a ƙasar Jamus. Haka kuma, ya yi aiki da Sashen Hausa na jaridar Daily Trust, ya kasance Mataimakin Editan jaridar Rariya, ya yi Editan gidan rediyon Hamada da ke Abuja, sannan ya shugabanci Sashen Hausa na gidan rediyon Kiss FM da ke Abuja, kafin daga bisani ya koma Radio Nigeria a matsayin Manager.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Nagode wa hukumomin Saudiyya da suka bani damar shiga Ka'aba - Tinubu - KAKAKI 24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet