Featured
Kotu ta yanke wa Umar hukuncin kisa bayan samun sa da laifin kashe uwa da ƴaƴanta 6 a Dorayi
Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11 da ke Bompai ta yanke wa Umar Auwal da Yakubu Dayyabu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci da ke Kano.
Arewa Updates ta rawaito cewa, Mai Shari’a Nasiru Saminu ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, bayan nazarin shaidu da hujjojin da aka gabatar a yayin shari’ar.
Kotun ta samu Umar Auwal, wanda aka fi sani da Breaker, da Yakubu Dayyabu, wanda ake kira Wawo, da laifin kashe mutanen bakwai a ranar 17 ga Janairu, 2026, inda ta yanke wa kowannensu hukuncin kisa ta hanyar rataya sau bakwai.
Haka kuma, kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai kan laifin haɗa baki da fashi da makami, yayin da ta wanke Isiyaku Yakubu tare da sallamarsa daga zargin haɗa baki da kisan mutanen bakwai.
