Connect with us

Labarai

Sokoto: Ƴan bindiga sun hallaka fiye da mutane 63 a kasuwar Goronyo

Wasu ƴan bindiga da ake zargin yaran gawurtaccen dan ta’addan nan Turji, ne sun kashe fiye da mutane 63 tare da jikkata wasu da dama a harin da suka kai babbar kasuwar Goronyo da ke jihar Sokoto.

Ƴan ta’addan da yawansu ya kai dari, sun mamaye kasuwar da misalin karfe 4:50 na yammacin jiya Lahadi dai-dai lokacin da mutanen kauyen ke harkokinsu na saye da sayarwa a cikin kasuwar inda suka bude musu wuta.

Rahotonni sun ce ‘yan bindigar sun kwashe kusan sa’o’i biyu sun cin karensu ba babbaka ba trae da kai daukin jami’an tsaro ba, wadanda ba a iya sanar da su harin ba sakamakon rufe hanyoyin sadarwa na yankin.

Jaridar Internet ta Solacebase ta ruwaito cewa majiya daga ƙaramar hukumar, ta ce an kirga gawarwaki 40 tun a daren jiya Lahadi.

Haka kuma, wasu daga cikin mazauna garin na Goronyo sun tabbatar da cewa tuni aka adana gawarwaki 62 a babban Asibitin Goronyo zuwa safiyar yau Litinin, baya ga wasu gawarwakin da danginsu suka tafi da su domin yi musu jana’iza.

Majiyoyin sun kuma ce akwai wasu da dama da har yanzu ba a gano su ba yayin da suke kokarin tsere wa ta hanyar shiga cikin ‘yan fashin dajin yayin da suke harbin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet