Labarai
Kaduna: Sojoji sun kashe fiye da ƴan bindiga 50
Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce, dakarun sojin Najeriya sun hallaka ƴan fashin daji fiye da 50.
Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar.
Sanarwar ta ruwaito cewa an yi nasarar hallaka ɓata garin ne a wani luguden wuta ta sama da aka yi musu a yankunan Saulawa-Farin Ruwa da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
Haka kuma ta ƙara da cewa yi musu luguden wutar ne a wasu hare-haren da gwamantin ta kaddamar na hadin-gwiwa.
Ta cikin sanarwar Aruwan ya ƙara da cewa dakarun sun kuma ƙona tarin makaman ƴan bindigar da kuma baburan da suke yin amfani da su wajen kai hari.
