Labarai
Bayan harin Bom: Hukumar NRC ta dakatar da sifurin jiragen ƙasa
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC, ta sanar da dakatar da ci gaba da aikin jiragen Kaduna zuwa birnin tarayya Abuja.
Dakatarwar na cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet yau Alhamis.
A cewar sanarwar, hukumar ta ɗauki matakin ne sakamakon matsalar tsaro.
Da yammacin jiya Laraba ne aka kai wa jirgin ƙasan da ya taso daga birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna, sai kuma da safiyar yau Alhamis aka sake kai wa wani jirgin hari shi ma a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.
