Travel
Shugaba Buhari ya dawo Najeriya
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauka a birnin tarayya Abuja daga ƙasar Saudi Arabia da ya je halartar taron zuba jari da kuma aikin Umara.
Rahotanni sun ce, shugaba Buhari, ya ya sauka ne da almurun wannan rana ta juma’a.
Haka kuma kafin tasowarsa sai da Shugaban ya yi Sallar Juma’a a Masallacin Ka’aba da ke birnin Makka.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kwanaki 5 a Saudi Arabia inda ya fara da zuwa birnin Riyadh daga nan kuma ya isa birnin Madina ya yi ziyara sannan ya je Makkah ya yi Umara.
Jaridar Internet ta Solacebase ta ruwaito cewa, jirgin fadar shugaban ƙasa mai ɗauke da shi da ƴan tawagarsa, ya bar filin jirgin saman Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah da misalin ƙarfe 3:45 agogon ƙasar.
