Rundunar ƴan sandan jihar Lagos, ta tabbatar da mutuwar mutane uku tare da wasu mutane 6 a wurin wani gini da ya rushe da tsakar ranar yau Litinin.
Rahotonni sun bayyana cewa, fiye da mutane 100 ginin ya runda da su.
BBC ta ruwaito cewa, wasu Shaidun gani da ido sun bayyana cewa cewa ginin ya rufta da mutane da dama da suka haɗar da ma’aikata da ƴan kwangila.
Haka kuma ta ruwaito cewa an jibge kayan aikin ceto da kuma na gano mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai a wurin.
