Labarai
Rikicin cikin gida: An hallaka gawurtaccen ɗan bindiga Dogo Gide
Rahotonni daga jihar Zamfara na cewa wani rikicin da ya kaure tsakanin ƴan bindiga, ya yi sanadiyyar kashe gawurtaccen jagoran ƴan bindigar nan Dogo Giɗe.
Wata majiya mai tushe ta ce, tun da fari rashin jituwa ne ya shiga tsakanin jagoran ƴan bindigar da mataimakinsa Sani Dan Makama wanda shi ne ya hallaka shi a dajin kuyanbana da ya haɗa garuruwan Dogon dawa a Zamfara da kuma yankin Birnin Gwari.
A watan Maris ɗin shekarar 2018 ne Dogo Gide ya hallaka riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan Buharin daji.
Dogo Giɗe dai ya shahara wajen aikata ayyukan fashi na tsawon lokaci a jihohin Zamfara da Neja da Kaduna da Katsina da kuma dazukan jihar Kebbi.
Ko a makon jiya sai da marigayin ya sanya wata doka ta hana sayarwa da kuma shan miyagun ƙwayoyi a yankunan da yake cin kare sa babu babbaka.
