Labarai
Ƴan sanda sun cafke mahaifin da ya yi tsafi da ɗansa
Rundunar ƴan sandan jihar Enugu ta ce, ta cafke wani uba bisa zargin sa da yin tsafi da ɗansa.
Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin jiya Alhamis.
A cewar rundunar binciken da ta yi kan mahaifin tuni ya amsa laifin kashe ɗan nasa.
Haka kuma ta ce, mutumin ya yiwa ƴan sanda jagora zuwa bakin wani rafi suka kama wani fasto mai shekaru 95 wanda ke da hannu a lamarin.
Rundunar ta kuma ce, ta gano gawar yaron a wurin da aka cafke faston har sun binne shi.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa, Kwamishinan ƴan sandan jihar ta Enugu Abubukar Lawal, ya bai wa umarci sashin binciken manyan laifuka na rundunar watau CID umarnin zurfafa bincike kuma da zarar sun kammala, su gurfanar da masu hannu cikin lamarin.
