Labarai
Neman ƙarin albashi: Ma’aikatan jirgin ƙasa sun tsunduma yakin aiki
Ma’aikatan hukumar zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya sun tsunduma yajin aiki yau Alhamis a wani mataki na neman ƙarin albashi da kula da rayuka da walwalarsu.
BBC ta ruwaito cewa tashoshin jiragen ƙasar sun inda gefe guda kuma ma’aikatan ke ɗauke da kwalaye suna zanga-zanga a tashar jirgin ta Idu da ke birnin tarayya Abuja.
Ma’aikatan sun ce za su fara yajin aikin na gargaɗi ne daga safiyar yau Alhamis har zuwa ranar Lahadi 21 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki.
Sai dai masana tattalin arziki na hasashen cewa yajin aikin na kwanaki 3 zai haifar wa Najeriya asara ta Fannin kuɗin shiga.
