Connect with us

Featured

Annobar Garkuwa Da Mutane: Halin da aka samu kai a Arewa – Nasiru Salisu Zango

Fitaccen ɗan jaridar nan da ke aiki da gidan rediyon Freedom a jihar Kano, Nasiru Salisu Zango ya bayyana takaicinsa akan irin halin da yankin Arewacin Najeriya ya ke ciki saboda sakaci da rashin kishi na shugabannin yankin.

Nasiru Salisu Zango ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na facebook, mai taken ‘Annobar Garkuwa Da Mutane. A cikin rubutun ɗan jaridar ya yi zargin yadda yankin arewacin Najeriya ke kokarin wani sansanin masu garkuwa da mutane wanda a zamanin baya a ke jiyo batun garkuwar a wasu sassan kasar nan.

Ga dai rubutun na Nasiru Salisu Zango:

Shekarun baya a FIM muke ganin ana garkuwa da mutane daga baya muka fara jin abin a yankin kudancin Najeriya sannu a hankali ya shigo arewa.

A baya matsalar kamar wasa-wasa amma ta samu gindin zama ta yi zaman ta a yankin mu, me ye matsalar ne?

A fahimta ta, babbar matsalar mu a arewa shi ne matsalar kirkirarren talauci da jahicin da shugabannin mu suka wanzar a yankunan mu, da kuma rashin shiga maganar ƴan uwan mu idan aka zalunce su. Yanzu yankin Arewa talaka ba shi da gata sai na Allah, kullum faftuka ya ke dan neman abin da zai ci, amma shugabannin mu kullum kirkirar tsare tsare suke da zasu ƙara ƙuntata masa.

Yanzu an kai gaɓar da abinci ma ya fara gagaraar dubban mutane, duk abin da ka ɗauka za ka iske an bar mu a baya.
Talauci yayi mana katutu, amma shugabannin mu da jagororin mu suna rige rigen hawa motocin miliyan tsababa, wannan magana ce bayyananiya ku duba irin motocin da suke hawa.

Noma da muke gadara da shi yanzu ya fara gagaraar mu abin kunya da takaici har yanzu da garma da fartanya ake noma, amma kullum an maganar cewa an inganta noma an samar da taki.
Ilimi kuwa sun bar makarantun mu sun lalace, azuzuwa a jagwalgwale abin ba kyan gani, dama ƴaƴansu ba a nan su ke karatu ba, dan haka ba su damu ba ko a jikinsu. Haka mu ke ta rayuwa kowa ya zuba ido, an kasa samawar da yankin mafita.

Yanzu ga matsalar garkuwa da mutane kowa yana cikin firgici amma shekara da shekaru an kasa shawo kanta, wai dan Allah meye laifin mu ne?

Mafi yawan shugabannin mu basa kishin mu, domin adalcin su baya ta shi sai wani namu yayi kuskure, Nnmadi Kanu babban ɗan ta’adda ne wanda yayi sanadiyyar kisan mutane, amma dattijan yankin sa ƙoƙari su ke a sake shi, duk da cin amanar ƙasa da yayi, amma Yunusa Yellow duk girman laifin sa bai kai na Kanu ba, yau an ma daina maganar sa.

Ba ina nufin Yunusa bai yi laifi ba, amma ina ga yadda aka tafiyar da maganar sa, ya kamata a ce an yi wani abu akansa, wannan dai ra’ayi na ne, amma na san ko kusa laifin sa bai kai na Kanu ba.

Da yawan shugabannin yankin mu sun Gaza sun bamu kunya, kuma sakacin su ne ya jefa mu cikin wannan hali. Allah ya samar mana da mafita, ya kawar da duk wanda ya hana ruwa gudu wajen cigaban yankin mu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet