Connect with us

Featured

Mata Da Sana’a: Burina in taimaki rayuwar mata a harkokin kasuwanci – Zainab Ɗanƙasa

A wannan makon filin mata da sana’a na kamfanin WhiteBlood Multimedia Service masu mallakin shafin jaridar Kakaki Hausa ya samu zarafin tattaunawa da wata matashiya mai suna Zainab Sani Mikail wacce aka fi sani da Xainerv Ɗanƙasa mamallakiya kuma jagorar kamfanin Ɗan ƙasa Dishes da ke jihar Kano a Arewacin Najeriya.

A cikin tattaunawar tamu da wannan matashiya ta bayyana mana yadda ta tsunduma cikin harkokin kasuwanci bayan kammala digirinta na farko a kan Library Science and Information Technology a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano. Zainab ta ce babban burinta a rayuwa shi ne taimakon mata da kuma ganin rayuwarsu ta inganta yadda za a dinga damawa da su a ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Hakazalika, Zainab Danƙasa ta ce ita kam yanzu Alhamdulillah domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, la’akari da yadda ta ke samun cigaba a harkokin kasuwancin da ta ke yi.

Ga dai yadda tattaunawar tamu ta kasance tare da ita:

Kakaki Hausa: Ko ya sunan matashiyar ƴar kasuwar?

Zainab: Sunana Zainab Sani Mika’il wacce aka fi sani da Xainerv Ɗanƙasa mamallakiya kuma jagorar kamfanin Ɗanƙasa Dishes.

Kakaki Hausa: Ko za ki sanar da masu karatu taƙaitaccen tarihin rayuwarki?

Zainab: An haife ni a unguwar ƙwalwa kwanar goda na yi makaranta daga matakin Primary har zuwa Jami’a inda na karanci Library and Information Science a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, haka kuma nayi makaranta islamiyya inda na sami kammala wasu daga cikin littatfan addini.

Kakaki Hausa: Wacce sana’ar ce ki ka yi fice?

Zainab: Kamar yadda kowa ya sani ina sana’ar girke girke wanda ya danganci abincin gargajiya, na zamani, ƙwalam da maƙulashe, abincin tarurruka da sauran su, haka kuma na kan taɓa sana’ar hijabai da takalma da kwalaben turare da sauran su.

Kakaki Hausa: Wacce nasara ki ka samu a wannan sana’a?

Zainab: Alhamdulillah an samu nasara mai yawa musamman yadda matsayin sana’ar ya ke samun sanji a kullum sai dai mu ce Alhamdulillah.

Kakaki Hausa: Waɗanne ƙalubale ki ke fuskanta a harkokin wannan sana’a?

Zainab: To a kowanne kasuwanci dole a fuskanci ƙalubale kamar haka ne muma a nan muna fuskantar ƙalubale sai dai Alhamdulillahi muna iya bakin ƙoƙari gurin shawo kan matsalolinmu. Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne wajen turawa abokan cinikayyar mu abinda su ke buƙata, sai kuma matsalar ƴan bashi.

Kakaki Hausa: Menene babban burinki a kasuwanci?

Zainab: Babban buri na a kasuwan ci shi ne na tallafawa matasa gurin samun ayyukan yi a ƙarƙashina tare da taimakawa iyaye da ƴan uwa da kuma abokan arziki. Haka kuma na kuma tsaya da kafafuna.

Kakaki Hausa: Menene abin da ki ka fi so?

Zainab: Abin da na fi so a rayuwa ta shi ne karamci da tsayawa akan gaskiya.

Kakaki Hausa: Menene abin da ba kya so?

Zainab: Bana son ƙarya bana son mai yin ta haka na bana son mutum mara darajta mutane.

Kakaki Hausa: Wacce kala ki ka fi so?

Zainab: A komai nafi son kalar fari sannan ina son Light blue da pink.
Kakaki Hausa: Menene kiranki ga matasa?

Zainab: Baban kira na ga matasa shi ne su tashi su nemi na kansu domin samun ingantacciyar rayuwa

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet