Connect with us

Featured

Gyara da ƙarin haske ga Murtala Sule Garo

Kwana uku da suka gabata kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo wanda ake yi wa kirari da kwamanda, a yi masa take da FIRE ya yi jawabi a wani taro a gaban jama’a.

A wajen taron ne Murtala GARO : ya ce Shekarau ya shiga kame- kame, ya shiga karume karume ya shiga fadar maganganu na rashin mutunci, to ba shakka jama’ar Kano za su maida masa martani. A cewarsa mutumin da ya karbi kudin makamai kuma hukumar EFCC ta tsare shi akan dukiyar al’umma,, ya sani Idan an ci zarafin gwamna ko iyalinsa, za su maida martani.

Kafin jama’ar Murtala GARO su maida martani, ga bayani da gyara.

Mallam Ibrahim Shekarau an gayyace shi EFCC a shekarar 2015, saboda ana zargin an yi amfani da gidansa an baiwa ‘yan jam’iyyar PDP kudaden zaben 2015 har naira miliyan 950, shi kuma a cikin kudin wai an bashi naira miliyan 25.

EFCC sun tsare Sanata Shekarau a ofishinsu har ya kwana, sannan suka tafi da shi gidansa na fadar Mundubuwa, suka yi bincike na kwakwaf tsawon awa shida. Sun birkice komai na gidansa da iyalinsa. Suka gama ba su samu komai ba sai kudi naira dubu dari biyu da hamsin da takwas. EFCC sun rike fasfo dinsa daga baya suka bashi kayansa ya ci gaba da harkokinsa

Bayan tsawon shekara da rabi sun kasa samun hujja, a ranar 23 ga watan Mayu 2018 EFCC suka gurfanar da shi a kotun ttarayya da ke Gyadi Gyadi karkashin Hajiya Zainab BageAbubakar .. An saka ranar sauraron sharia na farko na Mallam ranar 26 ga Yuni. 2018.
Bayan zaman kotu na farko aka jinkirta shari’a har wata hudu, sannan aka kawo sabon alkali Lewis Allagoa. Daga Oktoba 2018 har zuwa Satumba 2019 kotu ta zauna sau goma sha hudu. Ta yi hukunci cewa bayan shaidun EFCC gaba daya sun bada bahasinsu Sanata Mallam Shekarau yana da kes, lauyoyinsa suka yi jayyaya cewa zasu daukaka kara. An shekara guda da wata biyu ana musayar bayanai a kotun daukaka kara reshen Kano, a watan Nuwamba 2020 kotu ta kori karar, ta soke duk wani zargi ta wanke Shekarau. Aka bashi fasfo dinsa, kuma aka bude masa asusunsa na ajiya a banki, EFCC ta bashi hakurin bata masa lokaci.

Haji Murtala Kwamanda, gyaran a nan shi ne, ba a taba yin zancen kudin makamai ba, wannan kage ne, da kuma shaci-fadi wanda kake aiki da shi, ina son ka daina, ka rika yin bincike da hujja. Zaka rika jin kunya in kana magana cikin jahilci.

Abin da ya kamata ka sani a shekara takwas na mulkin Mallam Ibrahim Shekarau ya karbi kudade naira biliyan 487, amma bai taba kafa kamfani ba, bai taba bawa kansa kwangila ba, bai taba daukar dala daya ta gwamnati ba hakki, sannan ya sallami kowa a mulkinsa gwargwadon adalci.

Yau shekara 12 Sanata Shekarau ba ya gwamna, amma yana zaune lafiya da mutane a ko ina, a shekarunsa 66 ba a taba gabatar da shi ba a caji ofis ko kotu ko EFCC ko ICPC ko gaban sarki da laifin ya ci kudin jama’a. Ku bi a hankali, ina fatan ka fahimta!!! .

Bello Muhammad Sharada hadimi na Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet