Labarai
Tsugunne Ba Ta Ƙare Ba: Za a saki wasu Bidiyon badaƙalar Ganduje a karo na biyu
Wasu mutane a jihar Kano sun ce nan ba da jimawa ba za su sake fitar da wasu fayafayen bidiyon badakalar kudi da ke nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hancin dala.
Wata Majiya ta bayyana cewa a wannan karon faifan bidiyon ba daga Ja’afar Ja’afar mawallafin jaridar Daily Nigerian zasu fito ba, zasu fito ne daga wajen tsohon babban mashawarci na musamman ga Malam Ibrahim Shekarau, Honorabul Bashir Hayyatu Gentile.
Kamar yadda aka tsara, za a fitar da faifan bidiyo na farko da ya fi zafi kafin zaben 2023, kuma za a saki dukkan fayafayen badakalar bayan zaben 2023.
Hakazalika, Jaridar Neptune Prime ta bada da rahoton cewa akwai ƙarin mutane da kungiyoyi a cikin jihar Kano da suke bincike kan badakalar kudi na Gwamnan da matarsa. Idan dai za a iya tunawa, a ‘yan watannin da suka gabata ne dan gwamnan na farko, Abdulazeez ya kai karar mahaifiyarsa ga hukumar EFCC kan badakalar filaye.
Ya zuwa yanzu Ganduje wanda ya kai Ja’afar Ja’afar kotu ya an ci shi tarar Naira dubu ɗaru takwas, wanda ya riga ya biya Ja’afar Ja’afar wannan kudin har ya bayyana cewa ya bayar da kudin ne don taimakon masu rauni.
Al’amarin Bashir Gentile na zuwa ne bayan fadan siyasar Shekarau da Ganduje. Gentile wanda a yanzu shi ne babban mai ba shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Ahmed Lawal, kuma ya kasance mai biyayya ga Malam Ibrahim Shekarau a siyasance.
A kwana kwanan nan Anji Malam Ibrahim Shekarau cikin wani faifan bidiyo yana nasabta gwamnan da ”MAI CUSHE CUSHE”, lamarin da ya ja hankali sosai a siyasar jihar Kano.
Daga shafin Jarida Radio
