Labarai
Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi a Bauchi
Wata babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam’iyar APC a jihar, da ke biyayya ga ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu.
A ranar 16 ga watan Oktoba ne dai wasu ƴan jam’iyar su ka nuna rashin goyon baya da zaɓen shugabannin APC da Misau ya lashe, inda hakan ya janyo rabuwar kai a jam’iyar.
Da ga nan ne sai fusatattun ƴan jam’iyar su ka kai ƙara kotu, inda su ke roƙon a soke zaɓen sakamakon maguɗi da su ka ce an yi da kuma ƙaƙaba ɗan takara da wasu “ƴan siyasar Abuja” su ka yi.
A takardun ƙarar sun bayyana cewa wani Hassan Mohammed Sheriff ne ya shigar da ƙarar, inda ya nemi kotun da ta rushe shugabacin jam’iyar, ƙarƙashin Misau.
Ƙarar da a ka kai kotu ta haɗa da shugaban jam’iyar na riƙon ƙwarya na ƙasa, Mai Mala Buni, Shugaban Kwamitin Masu ruwa da tsaki na jam’iyar a Bauchi, Adamu Adamu da kuma mamba a kwamitin masu ruwa da tsaki, Yakubu Dogara, da sauran mutane 39.
Alƙalin kotun, Kunaza Hamidu, ya baiwa Misau da shi da sauran shugabannin jam’iyar da kada su ƙara nuna kan su a matsayin shugabannin jam’iyar har sai kotu ta saurari kowanne ɓangare ta kuma yanke hukunci.
