Connect with us

Labarai

PDP: Zamu Dawo Da Martabar Ƴan Najeriya A Zaɓen 2023

Jam’iyyar PDP ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya kudurinta na sake ginawa tare da dawo da martabar al’umma da ta rasa ta hanyar hadin kai, daidaito, adalci, bin doka da oda.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ne ya bada wannan tabbacin a wata liyafa ta musamman da gwamnatin jihar Benue ta shirya domin karrama shi a garin Makurdi na jihar ta Binuwai.

Sanata Ayu a wata sanarwa da ya fitar daga ofishin yada labaransa, ya koka da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin shugaba Buhari, saboda gazawarta na aiwatar da hanyoyin da za ta bi wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

A cewar sanarwar, “mulkin Shugaba Buhari ya kawo rarrabuwar kawuna, wahala, azaba da rashin yarda a tsakanin ’yan Najeriya, kuma, ya lalata mana mutunci, soyayya, amana, hakuri da juna a tsakanin addini da kabilanci.

“Kiyayya, karya da makirci sun mamaye fatanmu kuma sun haifar da zato da rashin hakuri a tsakanin mutane daban-daban a kasar.

“Sabon kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa, NWC, a karkashina, ta kuduri aniyar samar da shugabanci nagari a kasar nan, ceto da sake gina al’ummar kasar, domin samun dawwamammen canji mai inganci wanda zai samar da tsaro, daidaito, adalci, hadin kai da hadin kan ‘yan Nijeriya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet