Connect with us

Kasuwanci

Kotu a Kano dakatar da gina rumfuna a kasuwar ƙofar wambai

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta dakatar da Gwamnatin jihar gina shaguna a tsakiyar Kasuwa Wambai da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye.

Tun da fari, ƴan kasuwar ne su ka yi bore kan ginin shagunan bayan da gwamnati ta fara aza tubalin ginin.

Ƴan kasuwar sun koka cewa idan aka gina shagunan, to zai kassara cinikaiyar su saboda layin da gwamnatin za ta gine, shi ne babban layi da motoci su ke tsayawa su yi lodin kaya zuwa wasu sassan ƙasar nan.

Ganin cewa gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da duk koken da su ke yi na kar ta yi ginin, sai ƴan kasuwar su ka garzaya kotu domin a bi musu haƙƙin su.

Da ta ke sauraron ƙarar da ƴan kasuwar su ka shigar a yau Juma’a, Alƙaliyar kotun, A’isha Ya’u ta baiwa gwamnatin umarnin ta dakata da ginin har sai an saurari dukkan bangarorin biyu.

Ta kuma umarci dukkan bangarorin biyu da su dakata da ɗaukar wata matsaya a kan ginin.

Kotu ta ɗauki wannan mataki ne tun bayan karɓar ƙorafin da ta yi a ranar 17 ga watan Disamba.

Alkaliyar ta ɗage jin sauraron ƙarar zuwa 24 ga watan Janairu, 2022.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet