Connect with us

Labarai

Hatsarin Jirgin Kwale-kwale Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Jihar Niger

Akalla mutane bakwai ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a kauyen Zhigiri da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

An ce lamarin ya faru ne a lokacin da mutanen kauyen ke kan hanyar zuwa birnin Dnaweto; wani kauye da ke makwabtaka da kasar don gudanar da bikin suna da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi.

An kuma bayyana cewa wani mutum mai suna Muazu Babangida ya rasa matansa biyu da dansa guda a lamarin.

Kakakin Gamayyar Kungiyoyin Shiroro (COSA), Salis Saba Esq, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Minna, ya koka da cewa lamarin ya faru ne sakamakon samar da madatsar ruwa a tsakanin al’umma.

“Kafin gina madatsar ruwa ta Zungeru, tafiya tsakanin wadannan kauyukan biyu na kan kasa ne, kuma ba sa bukatar safarar ruwa, domin yankin ya kasance a bushe da kuma babura.

“Wannan yana daya daga cikin abunda ya haifarwa al’umma bisa gina madatsar ruwan. Ya zuwa lokacin da ake wannan rahoto, har yanzu ba a gano gawar daya daga cikin su a ruwan ba,” in ji Salis Saba.

Sai dai ya yi kira ga kungiyar HYPPADEC da ta gaggauta daukar mataki kan wannan mummunan lamari tare da samar da matakan tsaro da za su hada da rigunan rayuwa da sauransu don taimakawa mazauna wurin su dace da sabuwar hanyar rayuwarsu da kuma hana faruwar irin wannan abu a nan gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet