Featured
Niger: Wata Gobara Ta Tashi A Gidan Mai Sanadiyyar Fashewar Motar Tanka
Wata Motar Tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan man A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne da ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba.
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man fetur, lamarin da ya jefa jama’a cikin furgici kasancewar sauran tankunan mai maƙare suke da fetur.
Gwamna Zulum Ya Yi Alkawarin Farfaɗo Da Madatsar Ruwa Ta Biu
Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen don shawo kan lamarin, amma har yanzu wutar na ci gaba da yaɗuwa.
“Babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa, amma mutane sun tsere domin tsira da rayukansu,” in ji wani mutum, mai suna Abba Mohammed.
Ƙoƙarin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da hukumar kashe gobara a jihar Neja, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan labari.
