Connect with us

Addini

Mata Sun Fi Maza Himma Da Ƙwazo Wajen Neman Ilimi – Zainab Baraje

Babbar sakatariyar hukumar kasa da safayo ta jihar Kano Dr Zainab Ibrahim Baraje ta bayyana haka ne a tattaunawar ta da KakakiHausa a wajen taron Saukar Karatun Alkur’ani mai girma na Makarantar Adam Mai Agogo Islamiyya da ke Sharada phase 1 a jihar Kano.

Zainab Baraje ta ce abinda yasa ake yin karatun amma ake rasa tarbiyya shi ne saboda yawan al’umma, ga addinin a ko’ina amma zamani  ya hana neman sa, amma mafitar itace dai yin ilimin.

Baraje ta yi addu’a da fatan kowa a cikin iyalansa da unguwarsu ya zama mai kula da sanya idanu domin ganin gyaran ya tabbata.

A nasa ɓangaren shugaban wannan makaranta ta Adam Mai Agogo Islamiyya Malam Yahya Muhammad Adam ya ce an kafa Makarantar a 1998 da dalibai 3 kuma ta fara ne daga sorayen gidaje da kofar gida, Malam Tijjani shi ne ya samar da wannan Makaranta wacce ta ke da bangarori daban-daban.

Malam Yahya ya ce daga cikin nasarorin da aka samu shine yanda wasu dalibai suka sami shiga Kwaleji da shedar wannan Makaranta.

Ya kuma ce makarantar ta fara yaye dalibai ne a shekarar 2000 kuma wannan sauka da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata itace karo na 11, inda aka yaye ɗalibai 46 maza da mata.

Daga ƙarshe ya yi kira ga Iyaye da su rika sanya ido akan ‘ya’yansu domin shi Malami a cikin Makaranta ne kawai yake da iko akan Dalibi, kuma su rika bibiyar karatu da zuwa Makarantar ta su musamman a wannan lokaci.

Suma wasu Dalibai sun nuna matukar farin cikin su da ganin wannan rana.

Maryam Abdurrahman ta bayyana cewa wasa da rashin muhimmanta neman ilimin yasa Mata suke fin Maza yawa a wajen neman ilimi musamman a wajen sauka.

Shima Abdullahi Hamisu Umar wanda yana cikin Daliban da suka yi Saukar ya bayyana cewa neman kudi ne yasa mata suke fin su jajircewa wajen neman ilimi amma yanzu suma sun zage damtse.

Ya kuma ce akwai rashin jajircewar wasu Iyayen akan ƴaƴan su maza wanda hakan yana daga cikin abinda yasa Mata suka fi mazan zuwa Makaranta.

Usman Garba Alhassan kuwa cewa yayi, shi yana sana’a kuma yana zuwa Makaranta, inda ya yi kira ga Maza su yi kokari su koma Makaranta sannan sauran dalibai su jajirce da neman ilimi.

Sheikh Malam Abdullahi Uwais Abba Limanci  yana daga cikin mahalarta taron, kuma yace idan da tunani ya kamata idan mutum yana karatun Alkur’ani ya zama ya tsarkake zuciya da tufafi domin yana gaban Mala’iku ne a duk lokacin da yake karatun, kuma su kansu Malaman Makarantar su bar ladubban musulinci ko Malamai, shi yasa ana karatun amma kamar ba’a yi dabi’un al’umma basa nunawa.

Wakilinmu Nura Ahmad Hassan ya rawaito Malam Uwais na cewa daya daga cikin dalilan da yasa Matasa ba sa mayar da hankali wajen neman ilimi shi ne an ruguza rayuwar Matasanmu gaba ɗaya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet