Connect with us

Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Ta Dakatar Da Zanga-Zangar Da Za Ta Yi A Fadin Kasar Nan

Kungiyar Kwadago Ta Kasa NLC reshen jihar Kano ta sanar da Dakatar da tafiya zanga-zangar lumana da Uwar kungiyar ta shirya gudanarwa a fadin kasar nan ranar 27 ga watan Junairun da muke ciki.

Shugaban kungiyar NLC na jihar Kano kwamaret Kabiru Ado Munjibir ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taro gamayyar Shugabannin kungiyoyin sa kai da na Dalibai da na masu zaman Kansu da na Kate hakkin Dan Adam.

Kabiru Ado ya bayyana cewa a sakamakon janyewar batun cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi, Uwar kungiyar ta kasa ta yi taro a safiyar yau wanda aka tattauna batun kuma aka fitar da matsayar janye yajin aikin da kuma zanga-zanga a jihohi 36 na Kasar nan ranar 27 ga wannan wata, da kuma zanga-zanga ta Kasa a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Ya ce dalilin yin wannan zanga-zanga shi ne batun karin kudin man fetur kuma yanzu gwamnati ta janye kuma an sami matsaya, a don haka kungiyar ta Dakatar kuma ta jingine duk zanga-zangar da ta shirya.

Munjibir ya ce duk sanda gwamnatin tarayya ta sake yunkurin cire tallafin man fetur ko kara farashin man to kungiyar kwadago za ta sake shirya wannan zanga-zanga ta lumana da ma wasu abu uwa da zasu biyo baya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet