Connect with us

Labarai

Wani Hatsarin Mota Da Ya Faru Ya Yi Sanadiyyar Rayuka Da Dama A Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyar a sakamako faruwar wani munmunan Hatsarin mota a ranar Litinin 24 ga watan Janairu a garin Gamoji dake karamar hukumar Gaya ta jihar kano.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar mana da faruwar lamarin inda yace sun sami kira neman agajin ne daga bakin wani jami’in dan sanda mai suna Insifekta Ejede da misalin karfe 10:00 na safe.

Saminu yace bayan afkuwar hatsarin tsakani motar Homa bas mai lamba DRZ 830 XA wacce ta taho daga Bauchi sunyi karo da wata motar kasuwancin ta sharoon mai lamba DAL 846 YE wace ake kyutata zayon ta tashi daga kano ne wanda kuma ta kama da wuta nan take bayan afkuwar hatsarin.

Sannan yace hatsarin ya rutsa da mutane 22 kuma jami’an su da hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda sun sami nasarar ceto su, sai dai kuma biyar daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa dasu, an ceto su basa cikin hayyacin su inda a kai su Asibitin koyarwa na karamar hukumar Gaya inda likitoci suka tabbatar da sun mutu.

Kazalika ya kara da cewa sauran mutane 17 da wasu daga cikin su suka sami raunuka an kai su asibitin karamar hukumar Gaya dan basu kulawar likitoci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet